Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mohammed el-Baradei Yace Yana Da Kwarin Guiwar Za A Cimma Yarjejeniya Game Da Shirin Nukiliya Na Iran


Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya bayyana kwarin guiwar cewa za a iya cimma yarjejeniya da Iran wadda zata iya kawar da yin amfani da takunkumi dangane da shirin kasar na nukiliya da ake cacar baki kai.

Shugaban hukumar ta IAEA, Mohammed el Baradei, shine ya bayyana wannan yau litinin kafin taron da hukumar zata yi kan Iran, taron da zai iya zama harsashin daukar wani mataki kan kasar a Kwamitin Sulhun MDD.

El Baradei ya ce yana da kwarin guiwar za a iya cimma yarjejeniya a kan shirin makamashin nukiliya na Iran nan da mako guda. Ya ce ana kai gwauro da mari a fagen diflomasiyya domin maido da Iran da KTT a kan teburin shawarwari. Amma jami'an Amurka sun ce babu wata alamar dake nuna cewa a shirye Iran take ta bayar da hadin kai da kuma kyale sufetocin hukumar IAEA su binciki shirinta na nukiliya.

Tun da fari a yau litinin, shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran ya sake yin wani gargadin a Teheran yana mai cewa kasashen yammaci zasu haddasa wasu karin matsaloli ne kawai idan suka ci gaba da kara matsin lamba kan gwamnatinsa dangane da batun na nukiliya.

Amurka da KTT su na zargin cewa Iran tana kokarin kera makaman nukiliya a asirce, zargin da Iran ta ce shagulatin bangaro ne kawai.

XS
SM
MD
LG