Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Sojan Nijeriya Sun Ce An Kashe Sojoji Hudu Da Wani Dan Sanda Daya...


Jami'an soja a Nijeriya sun ce an kashe sojoji hudu tare da dan sanda daya a wani kazamin fadan da aka gwabza ranar laraba da 'yan ta-kife a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Wani kakakin rundunar sojojin ruwan Nijeriya ya ce 'yan ta-kifen sun yi kokarin sace wani jirgin ruwan mai ne a kogin Escravos, amma sai aka fatattake su. Jami'an gwamnati suka ce an kashe 'yan ta-kife uku.

Kungiyar 'yan ta-kife mai suna "Movement for the Emancipation of the Niger Delta" ko MEND a takaice, ta ce an kashe sojoji akalla bakwai a lokacin wani fada na tsawon mintoci 45 da bindigogi. Har ila yau sun ce jiragen ruwan kai farmaki na soja ne suka fara kai musu hari.

'Yan ta-kifen sun sace ma'aikatan man fetur 9 'yan kasashen waje a watan da ya shige, amma sun sako shida daga cikinsu. Sun ce ba zasu sako sauran ukun ba har sai an bai wa mutanen yankin Niger Delta karin kaso daga kudaden man fetur da kasar take samu.

Nijeriya ta fi kowace kasa a Afirka samar da man fetur, amma kuma tashe-tashen hankula cikin 'yan kwanakin nan sun rage yawan man da kasar take hakowa da kimanin kashi 20 daga cikin 100.

XS
SM
MD
LG