Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Idris Deby Na Chadi Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Dakarun tsaro na kasar Chadi sun ce sun murkushe wani yunkurin juyin mulkin da aka so yi cikin dare ma shugaba Idris Deby. Suka ce an yi kokarin harbo jirgin saman shugaban a lokacin da ya koma kasar daga wani taro a kasar Equatorial Guinea.

Wakilin Muryar Amurka, Nico Colombant, ya ce an girka sojoji a muhimman sassa na N'djamena, babban birnin Chadi a yau laraba, a bayan da aka samu rahotannin makarkashiyar juyin mulkin. Wasu sojoji ma sun hana motoci barin N'djamena ta kan wata muhimmiyar gada da ta doshi garin Khousri a bakin iyakar kasar da Kamaru.

An rufe dukkan layukan wayoyin mobayil ko salula na hannu a kasar.

Jami’ai a kusa da shugaba Idris Deby, wanda kwanakin baya ya kara sunan Itno a gaban sunansa, watau aka fara kiransa Idris Deby Itno, sun fadawa ’yan jarida cewar an kama wasu mutane, amma ba su yi karin haske ba. Sun dora laifin wannan yunkurin juyin mulki a kan wasu tagwaye masu suna Tom Erdimi da Timane Erdimi.

Wadannan tagwaye ’yan’uwan shi shugaba Deby ne, kuma tsoffin abokan huldarsa na siyasa da kasuwanci. Amma a yanzu sun shiga cikin sahun mutane masu yin tawaye ma shugaban na Chadi wadanda suka yi zango a bakin iyaka da yankin Darfur na Sudan suna neman shugaban da ya sauka daga kan mulki.

Kamar yadda mai bincike na Kungiyar Global Insight, Chris Melville, yake fadi ne, da yawa daga cikin wadannan ’yan tawaye ’yan kabilar shi kansa shugaba Deby ne wadanda suka kanainaye harkokin kasar Chadi. Mr. Melville ya ce, "Wadannan tagwaye ’yan gidan Erdimi suna da tasiri sosai a cikin ’yan jinsin Zaghawa wadanda suka kanainaye harkokin mulki a wannan gwamnati. Haka nan kuma su Zaghawan suna rike da manyan mukamai ko kuma sun taba rike manyan mukamai cikin rundunar soja kafin ’yan watannin da suka shige, a saboda haka idan ka auna irin arzikin da suka mallaka, zasu iya kalubalantar wannan gwamnati sosai a fagen soja...."

Ministan sadarwa na Chadi ya ce manyan mutanen da suka shirya juyin mulkin sun gudu a bayan da sojoji masu biyayya ga gwamnati suka fatattaki ’yan juyin mulkin. An ambaci wasu ’yan tawaye masu yin adawa da shugaba Deby suna fadin cewa an yi yunkurin juyin mulki, amma kuma wasu ne suka ci amanarsu suka fallasa su.

Wannan yunkurin juyin mulki ya zo a bayan da wasu manyan hafsoshin soja da aka tura domin su tattauna sasantawa da ’yan tawaye, su ma suka tube kayan soja na gwamnati suka canja sheka.

Tun daga lokacin da shugaba Deby ya samu agajin kudi daga waje domin gina bututun man fetur, yayi watsi da wasu dokokin da aka kafa musamman domin tabbatar da cewa wani bangaren arzikin man fetur da za a samu zai je ga kokarin kawar da talauci a tsakanin al’ummar kasar Chadi, yana mai fadin cewa kasar tana fuskantar matsalolin tsaro. Har ila yau ya rungumi akidar Tazarce, a bayan da ya sauya tsarin mulkin domin yin takara a karo na uku a zaben da za a yi a farkon watan Mayu.

XS
SM
MD
LG