Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Ruwa ya nitse a kan Teku a kamaru


Jami'an gwamnati a wani yanki na kasar Kamaroo sunce anajin cewa mutane wajen 130 sun rasa rayukansu a sakamakon nitsewar wani jirgin ruwa a wani yanki na gabar kudu maso yammacin kasar. Jami’anm sunyi kiyasin cewa akwai kimanin mutane 150 cikin wannan jirgin ruwa da ya taso daga gabashin Nigeria kan hanayarsa ta zuwa garin Gentin mai tashar jiragen ruwa a kasar Gabon. Jirgin ya kife ne a garin Kribi mai tasoshin jiragen Ruwa na kasar Kamaroo. Masinta ne suka sanar da hukumomin yankin bayan da suka ga kifewar jirgin. Rahotanni sunce mutane 23 ne kawai aka tsamo da sauran nunfashinsu. An sha samun hatsaruka da suka shafi ayyukan fito akan gabar Ginea a ‘yan shekaruna nan, inda Fasinjoji dankare cikin jiragen ruwa da basu da kyawawan hanyoyin sadarwa da kuma kayakin kiyaye lafiyar jirgi da fasinja suke nitsewa a teku.

XS
SM
MD
LG