Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hare-Haren Bama-Bamai Tare Da Yin Harbe-Harbe a Bagadaza...


An kashe ’yan Iraqi su akalla goma sha hudu, wasu fiye da tamanin suka ji raunuka, a hare-haren bam da harbe-harbe yau litinin a Bagadaza.

Bama-baman da aka dana cikin mota har bakwai sun tashi suka kashe mutane akalla 8. Bama-baman sun tashi a kusa da ma’aikatar lafiya, da wata jami’a da kuma wasu unguwannin birnin. An kashe wasu ’yan Iraqin su shida a harbe-harbe.

Wadannan hare-haren sun wakana a daidai lokacin ad sabon firayim minista Jawad al-Maliki yake kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Tun da fari a yau litinin, an koma ga zaman shari’ar Saddam Hussein da wasu mutane bakwai domin sauraron shaida daga bakin wasu kwararru kan rubutu wadanda suka ce sa hannun Saddam ne a kan takardun iznin kashe ’yan Shi’a fiye da dari da arba'in a kauyen Dujayil a 1982. Daga nan kotun ta dage ci gaba da zama har sai ranar 15 ga watan Mayu.

XS
SM
MD
LG