Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nepal Ta Yi Zamanta Na Farko Cikin Shekaru Hudu


Majalisar dokokin Nepal ta yi zamanta na farko cikin shekaru kusan hudu, a bayan da zanga-zangar makonni ta tilastawa sarki Gyanendra ya saki ikon mulkin da ya kwace, ya maido da mulkin dimokuradiyya.

An fara zaman majalisar dokokin na yau Jumma’a tare da yin shiru na tsawon minti daya domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a zanga-zangar nuna kin jinin sarki tare da neman kafa dimokuradiyya.

A waje, dubban ’yan zanga-zanga sun kewaye kofar shiga majalisar dauke da tutoci su na rera wakoki domin matsin lambar ganin an rubutawa kasar sabon tsarin mulki.

Firayim ministan da aka nada, G.P. Koirala, bai halarci zaman majalisar na yau ba a yayin da wakilai suka gana cikin wannan gini na majalisa da aka kawata shi sosai a tsakiyar birnin Kathmandu.

Tsohon dan siyasar mai shekaru 84 da haihuwa, wanda aka yi niyyar rantsarwa, yana fama da laulayi, kuma mukarrabansa sun ce wani viwon dake damunsa a huhu ya sa aka dage shirin rantsar da shi.

Jiya alhamis da maraice sarki Gyanendra ya nada Mr. Koirala a bayan da shi sarkin ya mika ikon siyasa ga jam’iyyu bayan da aka shafe makonni ana zanga zangar nuna kin jinin kwace ikon mulkin kasar baki daya da yayi.

’Yan tawaye masu akidar Mao <b>(Tse Tung, tsohon shugaban kwaminisanci na kasar Sin)</b>, wadanda suka yi shekaru goma su na yin tawaye, sun bayar da sanarwar tsagaita wutar watanni uku a jiya alhamis, a bayan da Mr. Koirala ya tabbatar musu da cewa zai shirya zaben majalisar da zata zana sabon tsarin mulki.

XS
SM
MD
LG