Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Darfur Sun Ce Lallai A Yi Gyara Ga Daftarin Yarjejeniyar Zaman Lafiya


’Yan tawaye na yankin Darfur a kasar Sudan sun nace kan lallai sai a yi gyara ga daftarin yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnatin Sudan ta ce zata sanyawa hannu. Masu magana da yawun kungiyoyin tawaye biyu na Darfur sun sake nanata wannan bukata yau litinin a yayin da ake ci gaba da tattaunawar neman zaman lafiya a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta kara wa’adin kwanaki biyu, ko sa’o’i 48, a bayan da gwamnati da ’yan tawaye suka kasa daidaitawa ya zuwa wa’adin da aka shimfida musu na jiya lahadi. Amurka ta bukaci Kungiyar da ta kara wannan wa’adi domin a yi kokarin cimma daidaituwa a bayan shawarwarin shekaru biyu.

’Yan tawayen na Darfur sun ce su na bukatar wakilci mai karfi a gwamnatin tarayyar Sudan, da kuma ka’idoji masu kyau na shigar da dakarunsu cikin rundunar sojojin Sudan.

An yi kiyasin cewa mutane dubu dari da tamanin sun mutu a cikin shekaru ukun da aka yi ana gwabza yaki a tsakanin ’yan tawaye da sojojin gwamnati da kuma ’yan bangar da gwamnati ke goyon baya a yankin na Darfur. Mutane fiye da miliyan biyu sun gudu daga gidajensu ala tilas.

XS
SM
MD
LG