Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakariya Muossawi zai karasa zamaninsa a gidan sarka...


Ayarin Amirkawa dake taya Alqali yanke hukunci sun yankewa Zakarias Moussaui (Musawi) mutumin da aka samu da laifin hada baki da 'yan ta'adda a harin da kungiyar Alqa'ida ta kaiwa Amirka a ranar 11 ga watan Satumba na shekara ta dubu biyu da daya hukuncin daurin rai da rai ba tare da samun damar a sake nazarin hukuncin da aka yanke masa ba.

Gungun masu taya alkali yanke hukuncin su goma sha biyu, a kotun tarayyar Amirka dake zama a jahar Virginia, sun shafe kwanaki bakwai suna shawara akan irin hukuncin da za su yankewa Mr. Moussaoui dan shekaru 37 da haifuwa na daurin rai da rai ko kuma a kashe nan take.

Alkalin kotun tarayya Leonei Brikeman ne gai fada wa Moussaoui hukuncin da ka yanke masa a ranar Alhamis hudu ga watan mayu. Ada dai wasu mata uku sun yanke hukuncin cewa Zakarias yana da laifi na akallan mutuwar mutun ko guda daga cikin wadanda suka mutu a sakamakon wancan harin. Don haka sukace ya cancanci a yanke masa hukuncin kisa.

Shi dai Moussaoui (Musawi) shine mutun daya tilo da Amirka ta yankewa hukunci a dangane da harin watan Satumba. A bara ya amsa cewa ya aikata laifi a zargi shidda da ake masa na hada baki domin kawo wannan harin.

XS
SM
MD
LG