Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai tura wakili  a yankin Timor ta Gabas


Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce zai tura wani wakili zuwa Timor ta Gabas, inda fitina ta kara muni a tsakanin sojojin gwamnati da tsoffin sojojin da suka yi yakin kwatar ’yancin kasar. Wani kakakin babban sakataren ya ce a duk tsawon yau alhamis ya tuntubi shugabannin yankin domin sanin takamammen halin da ake ciki. A halin da ake ciki, zaratan sojojin kasar Australiya su kimanin 150 sun isa Timor ta Gabas a yau alhamis. Firayim minsitan Australiya, John Howard, ya ce zai gaggauta tura sojoji kimanin dubu daya da dari uku zuwa yankin a saboda yadda al’amura suke kara tabarbarewa a kasar. A rana ta uku a jere, an goce da fada da bindigogi a tsakanin sojojin gwamnati da tsoffin sojojin a Dili, babban birnin kasar da kuma wasu wuraren. An kashe mutane akalla biyu yayin da ’yan kasashen waje suke arcewa daga wannan birni.

XS
SM
MD
LG