Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayiministan Gabashin Timor yaki ya sauka...


Firayi-Ministan kasar Gabashin Timor, mari alkatiri ya amince akan a tura masu aikin bincike na kasa da kasa aka su bincike musabbabin tashin hankalin da ya rikita kasarsa tun cikin watan jiya. Duk da haka yace ba zai sauka daga karagar mulkin kasar ba

A Daidai wannan lokacin da yake samun Karin matsin lamba akan ya sauka daga mukaminsa, firayiministan gabashin Timor da ruwan rikici ke naman cinyewa, Mari Alkatiri ya ki sauka daga mukamin nasa yana mai cewa an zabe shi ne ta fuskar demokradiyya. Bayan wata ganawa da wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya yi yau Laraba tare da ‘yan tawayen dake boye a kan duwatsun dake kusa da birnin Dili babban birnin kasar, wakilin na Majalisar Dinkin Duniyar, Sukehiro Hasewaga ya ce Mr Alkatiri ya amincewa masa akan ayi wani bincike na hadin guiwa tsakanin jami’ai da kuma hukumomin kasar.

Ya ce ayi bincike da zai kunshi ‘yan aikin bincike na kasa da kasa da kuma wasu lauyoyi. Kasar gabashin Timor ta fada cikin wani gagarimin tashin hankali bayan da Mr Alkatiri ya kori sojojin kasar dari shidda daga cikin ayarin sojin kasar dubu da dari hudu bayan da suka yi watsi da aikinsu bisa zargin da suka yi na nuna musu banbanci da kuma rashin kyawun yanayin aikinsu.

Wannan mataki da fiyayi ministan ya dauka shi ya janyo tashin hankali a babban birnin kasar Dili inda‘yan daba daga yankunan gabashi da yammacin kasar dauke da makamai suka yi arangama da juna akan titunan birnin suna kwasar ganima daga kantuna kuma suka rika kona gine–gine. Ana ganin 'yan bangaren yammacin kasar a matsayin mutanen da suka goyi bayan kasar Indonesia a lokacin da ta shafe shekaru Ashirin da hudu tana mulkin mallaka a kasar, sannan su kuma na yankin Gabashin kasar su suka yi yakin neman ‘yancin kasar daga hannun kasar Indonesia.

‘yan kasar da dama suna zargin firayi-minstan kasar da laifin kasa magance matsalar rikicin kasar. Wannan rikici ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya su dubu biyu da dari biyar daga kasashen Australia, da New Zealand, da Malaysia da kuma Portugal zuwa Birnin Dili bayan da gwamnatin kasar ta bukaci taimakon Majalisar. Manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a yankin gabashin Timor, Ian Martin ya bar birnin Dili a yau Laraba ya ce zai shawarci kwamitin sulhu na MDD ya amince da kafa rundunar ‘yansanda Majalisar a kasar. Kafin tashinsa, ya ce kusan kowa a yankin ya yi imanin cewa yanzu lokaci yayi da Majalisar za ta taka muhimmiyar rawa nan take, na kawo zaman lafiya a yankin. Kimanin mutane dubu biyu ne su ka yi zanga-zanga suna kira ga fiyayiministan kasar akan yayi murabus jiya Talata sannan a kira ayi zabe

.

XS
SM
MD
LG