Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kotun Islama ta kasar somaliya, ya gargadi gwamnatin kasar.....


Shugaban kotunan kasar Somaliya ya gargadi gwamnatin kasar akan kadda ta kuskura ta bari a tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen kyetare zuwa kasar su.

Sheik Sharif Ahmed ya ce ba za'a ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin tunanan Islam na kasar sai lokacin da gwamnatin kasar ta yi watsi da burinta na neman a tura sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashen Uganda da Sudan ta hannun kungiyar raya kasashen gabashin Afirka tukuna.

A yau Litinin, Majalisar rikon kwaryar kasar Somalia ta za ta yi zaman shawarwari a game da batun tura sojijin kiyaye zaman lafiyar. Ita wannan gwamntin rikon kwarya wacce bata da karfi sosai tana son maida helkwatarta daga garin Baidoa zuwa birnin Mogadishu.

Mayakan sakai masu goyon bayan kotunan Islamar kasar, sun kwace ikon birnin Mogadishu daga hannun shugabannin tarayyar kungiyoyin masu kyamar cusa addini a harkar mulki, bayan da suka shafe watanni hudu suna fafata yakin da ya ci rayukan mutane dari uku da hamsin.

XS
SM
MD
LG