Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a tura Charles Taylor kasar Neitherlands don shari'a...


Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bada umurni akan a maida tsohon shugaban kasar Liberia Chrles Taylor zuwa birnin Hague gaban kotun kasa da kasa domin ta masa shari’a laifukan yaki da ake tuhumarsa da aikatawa.

A yau kwana guda bayan da kasar Birtaniya ta ce za ta ajjiyeshi a gidan kurkuku a kasar idan har an sami Mr Taylor da laifi a zargin da ake masa, k gwamnatin kasar Neitherlands ta ce ta kammala shirye-shiryen karbansa daga hannun kotu na musamman dake zama a kasar Saliyo. A yanzu haka Mr. Taylor yana hannun kotun kasa da kasa ta musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a kasar Saliyo wacce ta zarge shi da aikata laifuka 11 da suka shafi ayyukan rashin imani a lokacin yaki. Jami’an kasar Saliyo sun roki Majalisar Dinkin Duniya akan ta janye shari’ar nasa daga kasarsu zuwa birnin Hague saboda fargaban irin tashin hankali da shari’ar za ta janyowa a tsakanin kasashen yammacin Afirka.

Laifukan da ake tuhumar Charles Taylor sun hada da goyon bayan ‘yan tawayen kasar Saliyo wadanda aka zarge shu da laifin yiwa mata fyade da sare hannayen mutane da kuma kasha fararen hula haka siddan a lokacin da aka shafe shekaru 11 ana yakin basasa a kasar. Haka kuma ana tuhumarsa da laifin ingiza yaki a kasashen Liberia da Saliyo. Wani lokacin a farkon wannan shekara ne aka kaishi kasar Saliyo bayanda gwamnatin Najeriya ta soke mafakar siyasar da ta ba shi, daga nan ta koreshi daga kasar.

XS
SM
MD
LG