Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar kasashen Afirka da kasashen Turai  suna son tura sojin kiyaye zaman lafiya Somaliya


Kungiyar Tarayyar kasashen Afirka da kasashen yammacin duniya suna kokarin ganin shirintura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen waje a kasar Somalia. ‘Yan aikin diplomasiya suna ganawa a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, a yau Litinin domin cimma yarjejeniyar tura wani ayarin da zai share fagen tura sojojin kiyaye zaman lafiya. Manzon kasashen Turai a zauren Taron, Tim Clark yace ‘yan aikin Diplomasiyya suna jin tsoron cewa halin da ake ciki a wannan kasa ta gabashin Afirka yana iya kazancewa nan take imba an dauki mataki na hanzari ba.

Mayakan sa kai masu goyon bayan kotunan kasar, sun kwace ikon birnin Mogadishu da wasu sassan kasar daga hannun shugabannin kungiyoyi masu adawa da cusa addini a harkokin mulki. Kotunan kasar somaliya dai sun nuna damuwarsu game da tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen waje zuwa kasar.

Jiya Lahadi mayakan sa kai masu goyon bayan kotunan kasar suka dauki matakinsu na baya bayan nan inda suka kafa dokokin shari’a a kasar, yayinda hakan ta sa suka rufe jidagen Sinima a garin Jowhar. A halin da ake ciki kuma shugaban kotunan Islama na kasar Sheik Sharif Ahmed ya zargi kasar Ethopia da laifin tura sojoinsu su tsallaka kan iya su shiga kasarsa, zargin da tunin kasar Habashan ta musanta.

XS
SM
MD
LG