Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Iraqi Sun kashe Sojojin Amurka Biyar


’Yan tawaye a kasar Iraqi sun kashe sojojin Amurka biyar. Jami’an Amurka sun ce an hallaka sojojin kundumbala hudu a wasu hare-hare biyu ranar talata a lardin Anbar dake yamma da Bagadaza. Sojan Amurka na biyar ya mutu lokacin da wani bam da aka boye a gefen hanya ya tashi a kudu da birnin Bagadaza jiya laraba.

A wani labarin kuma, babban lauyan Saddam Hussein, Khalil al-Dulaimi, ya ce Saddam da wasu mutanen da ake tuhuma da dama sun fara yajin cin abinci domin nuna rashin jin dadin yadda ba a tsaron lafiyar lauyoyin dake kare su. Jiya laraba, wasu ’yan bindiga sun sace daya daga cikin manyan lauyoyin Saddam, Khamis al-Obaidi, suka kashe shi.

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka yayi tur da kisan, amma kuma ya ce lauyan da aka kashe ya ki yarda da tayin da Amurka ta yi masa na ba shi kariya.

A wani gefen kuma, babu takamammen bayanin yawan ma’aikatan masana’antar da har yanzu ake rike da su a bayan da aka sace su jiya laraba a Taji dake arewa da Bagadaza. Kafofin labarai sun fada jiya laraba cewar an sace ma’aikata har tamanin da biyar daga wannan tsohuwar masana’antar soja. Amma kuma wasu jami’an Iraqi sun ce mutanen kimanin talatin ne, kuma an sako da yawa daga cikinsu.

XS
SM
MD
LG