Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Minista Tony Blair Na Britaniya Zai Bayar Da Sanarwar Kafa Wani Babban Kwamiti...


A yau litinin firayim minista Tony Blair na Britaniya yake shirin bayyana kafa wani babban kwamiti wanda zai sanya idanu a kan alkawuran da kasashe masu arziki suka yi na kawar da talauci daga nahiyar Afirka.

Ofishin Mr. Blair ya ce babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, shi ne zai shugabanci wannan kwamitin da aka sanyawa suna "Kwamitin Ci Gaban Afirka." Sauran wakilan kwamitin zasu hada har da attajiri Bill Gates na Amurka mai kamfanin kayayyakin sarrafa Kwamfuta, da shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya, da kuma shahararren mawakin Rock, Bob Geldof.

Jami'an Britaniya suka ce Mr. Blair yana shirin bayyana cewa sanya idanu da bin sawun alkawuran da kasashen kungiyar G-8 suka yi aiki ne na dindindin. Ana sa ran zai bayyana cewa an samu ci gaba wajen rage talauci a Afirka, amma kuma har yanzu da sauran aiki.

A lokacin taron kolin da suka yi bara a Gleneagles a Scotland, shugabannin kungiyar kasashe masu arzikin masana'antu a duniya, G-8, sun yi alkawain bayar da karin dala miliyan dubu hamsin ga kasashe masu tasowa nan da shekarar 2010. Kimanin rabin wannan kudi za a bayar da shi ga kasashen Afirka.

XS
SM
MD
LG