Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

P.ministan Hamas, jam’iyyar da ke shugabancin gwamnatin Palesdinawa ya ce, yana aiki tukuru domin kawowar karshen tashin hankalin


Prime ministan Hamas, jam’iyyar da ke shugabancin gwamnatin Palesdinawa ya ce, yana aiki tukuru domin kawowar karshen tashin hankalin da ya biyo bayan garkuwa da wani sojan Israila da mayakan Palesdinawa suka yi.

Duk da haka, PM Ismail Haniyeh ya ce, matakin maida martanin da sojojin Israila ke yi da gurin ‘yanto sojan Israila yana kara dagula al’amarin

Dakarun Israila na ci gaba da kai hare hare ta sama da na atilare a kan Zirin Gaza, amma sun dakatarda kai harin sojan kasa a bisa rokon gwamnatin Masar.

XS
SM
MD
LG