Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta gabatar Da Jawabin Farko Dangane Da Gwaje-Gwajen Makamai Masu Linzami Da Ta Yi


Koriya ta Arewa ta gabatar da jawabinta na farko dangane da gwaje-gwajen makamai masu linzami da ta gudanar ranar laraba, inda ta bayyana su a zaman wadanda suka yi "nasara" ta kuma lashi takobin gwada wasu a nan gaba.

Koriya ta Arewa ta ce zata yi amfani da karfin soja a kan dukkan matakan da wasu kasashen waje zasu so dauka domin hana gwaje-gwajen.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta bayar a yau alhamis, ta ce an gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzamin ne domin karfafa tsaron kai.

An ambaci ma'aikatar tsaro ta Koriya ta Kudu tana fadin cewa watakila Koriya ta Arewa tana shirin kara harba wasu makaman masu linzami a bayan da ta yi gwajin harba guda bakwai a ranar laraba, cikinsu har da wani mai cin dogon zango.

Wani babban jami'in gwamnatin Japan ya ce kasarsa ba ta tsammanin Koriya ta Arewa zata sake gwajin wani makami mai linzami dake cin dogon zango.

Shugaba Bush ya tattauna wannan batu ta wayar tarho da shugabannin Koriya ta Kudu da Japan.

Mr. Bush da firayim minista Junichiro Koizumi na Japan sun yarda zasu yi kokarin ganin Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin sanya takunkumi a kan Koriya ta Arewa. Ministan sake hada kasashen Koriya a gwamnatin Koriya ta Kudu (Lee Jong-seok) ya ce kasarsa zata ci gaba da gudanar da ayyukan hadin kai na kasashen duk da wannan gwajin makamai masu linzami.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Condoleeza Rice, tana tuntubar takwarorinta na gungun kasashen nan shida dake tattaunawar nukiliyar ad ta cije, cikinsu har da na kasashen Sin, Japan, Rasha, da Koriya ta Kudu.

Babban jami'in dake wakiltar Amurka a shawarwarin, Christopher Hill, zai isa Asiya nan gaba a yau alhamis domin tattauna gwaje-gwajen makamai masu linzamin da makwabtan Koriya ta Arewa.

XS
SM
MD
LG