Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Nigeria sun ce 'yan bindiga sun kai hari a kan wata rijiyar hakar mai dake tsakiyar ruwa..


Jami’an Najeriya sunce yan bindiga sun kai hari kan wata rijirayar hakar mai dake tsakiyar ruwa suka sace wani jami'in tsaro. Wani kakakin sojan ruwan Najeriya ya fada a yau Alhamis cewa ma haran daga yankin Sangana sun kai harin ne ranar Laraba. Ya ce satar jami’in tsaro ya aukune lokacinda maharan ke kokarin tserewa. Kakakin ya ce yan bindigan sun zargi kamfanin dake hakar mai a wannan rijiyar da laifin saba alkawari da ta yi wa mazauna yankin. Kamfanonin hakar mai a yankinda ke fama da talauci duk da arzikin mai,a yankin Niger Delta ba kasa fai su ke cika alkawarin yarjejeniya tsakanisu da al’umar yankin na samar da aiki da kuma habaka yankin ba.

Jami’an Najeriya ba su ce ko akwai wata alaka tsakanin wadanda suka kai hari a jiya Laraba da kungiyar 'yan takifen wadanda suke kai jerin hare hare kan ma'aikatun hakar mai a yankin. Yan tawayen sun bukaci a baiwa al’umar yankin Karin kaso na arziki mai dake fitowa daga yankin.

XS
SM
MD
LG