Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani sabon artabu a birnin Mogadishu ya ci rayuka Ashirin da daya


Wani sabon fada ya kaure a birnin Mogadish inda mayakain sa kai masu goyon bayan kotunan Islama da kuma masu biyayya ga shugabaninin jinsunan kasar a ranar Lahadi. Asibitocin birnin Mogadishu sunce akallan muntane goma sha takwas aka kashe a yau Litinin bayan fadar jiya Lahadi da yayi sandadiyyar mutuwar mutane Ashirin da Daya.

Darurwan mazasuna yankin kudancin birnin Mogadishu sun arce daga gidajensu a lokacin da kungiyoyin mayakan sakai suka rika musayar wuta da bindigogin igwa. Wani shugaban mayakan sa kai Abdi Awale Qaybdiid ya ki ya bada kai ga hukumomin Islamar kasar wadand asuka rike da akasarin yankin babban binrin kasar. Qaybidid yana cikin wata kungiyar kawance masu adawa da cusa addini a harkokin mulki da aka wargaza.

A halin yanzu kuma shugabannin gwamantin rikon kwaryar kasar Somaliya da Majalisar Dinkin Duniya da ke marawa baya, sun ce ba zasu gana da jami'an hukumar kotunan islamar kasar masu tsananin ra'ayi ba. Dama dai ita gwamnatin ta shirya zata zauna tattaunawa tsakaninta da kotunan kasar masu iko a kasar Sudan.

Kotunan kasar Somaliya dai sune ke jagorancin kugiyoyin kasar da suka kwace ikon yankunan kudancin kasar a wannan shekara. Kotunan sun so su kama gwamantin Islama, to amma gwamnatin rikon kwaryar kasa ta ki amincewa. Ita dai gwamnatin bata da wani ikon kirki in banda a garin Baidowa inda take zaune.

XS
SM
MD
LG