Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Ce Jinsuna Dabam-Dabam Na Kwayar Cutar Murar Tsuntsaye Sun Shiga Nijeriya


Masana kimiyya sun ce sun gano shaida daga Nijeriya cewar sau da dama kwayar cutar murar tsuntsaye H5N1 mai kisa ta shiga kasar, ba a karo daya kawai ba.

Kwararru sun fada a cikin mujallar Nature wadda ta fito ranar alhamis cewa sun yi imani jinsuna da dama na kwayar cutar murar tsuntsayen sun shiga cikin kasar a lokuta dabam-dabam, ba wai jinsin kwayar cutar guda daya tak ce ta shiga ta yadu a cikin Nijeriyar ba.

Masana kimiyya suka ce wannan sabon lamarin da suka gano yana iya kara wahalar yunkurin dakile yaduwar wannan cuta.

Masana kimiyya sun auna samfurin tsuntsayen da suka kamu da cutar a gonaki da dama a kasar, suka kuma gano cewar akwai jinsuna dabam-dabam na kwayar cutar wadanda ba su yi kama da juna ba.

Binciken nasu bai gano ko tsuntsaye masu yin kaura kowace shekara ne suka kai kwayar cutar cikin Nijeriya ba, ko kuma dai sun shiga ne ta hanyar tsuntsaye da jama’a suka sayo daga kasashen waje.

Nijeriya ita ce kasar Afirka da ta fara fuskantar ukubar cutar murar tsuntsaye a lokacin da aka gano kwayar cutar cikinta a watan Fabrairu.

XS
SM
MD
LG