Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Tasiri Ko Rashin Tasirin Yankin Middle Belt A Harkokin Siyasar Arewa?


A wannan karon, shirin "Tsaka Mai Wuya" ya tabo batun yankin nan na tsakiyar arewacin Nijeriya da ake kira "Middle Belt" a turance. A saboda kasancewar yankin tamkar gadar ad ta hade arewa da kudu, da kuma irin launi na kabilu da addinai dake cikin wannan yanki, har yanzu ana jayayya kan irin rawar da zai taka a harkokin siyasa.

A cikin wannan shiri da aka kasa gida biyu, Aliyu Mustapha ya shiga tsakani a muhawarar da aka tabka tsakanin tsohon minista Paul Unongo da Bashir Baba, sakataren farko na Kwamitin Turaki wanda ya rikide ya koma Kungiyar Tuntubar Juna ta Arewa.

XS
SM
MD
LG