Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ahmed Sani Yeriman Bakura, Shugaban Nijeriya A 2007?


Masu yin hamayya da Ahmed Sani Yeriman Bakura, gwamnan Jihar Zamfara, su na nuna adawa da shawarar da ya yanke ta tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2007.

Hujjar 'yan hamayyar ita ce shi gwamnan bai tabuka wani abin kirki ga al'ummar Jihar Zamfara ba, ta yaya ne zai iay jagorancin Nijeriya?

Magoya bayansa suka ce, ai babu wani wanda ya dace ad ya jagoranci kasar idan ba Yeriman Bakura ba.

A wannan muhawara da aka tabka a kan wannan batu, sakataren gwamnatin Jihar Zamfara, Hussaini Moriki, wanda yake wakiltar jam'iyyar ANPP, shi ne ya kalubalanci Kabiru Moyi Birnin Magaji, sakataren jam'iyyar PDP a Jihar Zamfara.

XS
SM
MD
LG