Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila ta tura sojojinta zuwa kasar Lebanon


Isra’ila ta tura sojojinta zuwa yankin kudancin kasar Lebanon domin wani kokari na kwato sojojin kasarta biyu da mayakan sa kai na kungiyar Hezbullah suka kame a yau laraba da safe. Isra’il ta kuma jefa Bam akan wata gada da hanyoyi a kudancin Lebanon domin ta hana ‘yan Hezbullah din wucewa wani waje da sojojin da aka sace mata. Jami’an tsaron Lebanon sunce hare haren Isra’ilan sun kashe fararen hula ‘yan kasar akallan biyu.

Mayakan sa kai na Hezbullah sun kama sojojin Isra’ila biyu a lokacin da suka yi wata musayar wuta ta kan iyaka abinda ya janyo mutuwar akallan sojojin Isra’ila shidda. Kungiyar ta ce ta lalata wani tankin yaki na sojan Isra’ila bayan da ya tsallaka ta kan iyaka ya shiga kasar Lebanon.

Firayi-ministan isra’ilan Ehud Olmert ya kira wani taron gaggawa na majalisar ministocinsa domin su tsaida shawara akan matakin da za su dauka na nan gaba. Ya kirayi wannan kame sojojinsa da Hezbullah ta yi a matsayin “tsokanar yaki daga Lebanon” Rahotanni sun ce Isra’ila ta kira sojojinta masu zaman jiran ko ta kwana akan su dawo su sa kaki don jira umurni. Ita kuma kungiyar Hezbullah, cikin wata sanarwa da ta bayar ta ce a shirye take ta fara shawarwarin da Isra’ila akan batun musayar fursunoni, sai dai bata fitod fili akan ko fursunoni ‘yan kasar Lebanon kona Palasdinu take so Isra’ila ta sako ba. Wannan shine karo na farko da Isra’ila ta tura sojoji masu yawa zuwa kasar Lebanon tun daga lokacin da ta fice daga kasar a shekara ta dubu biyu. (2000)

A birnin Alqahira, mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka David Welch ya bayyana kama sojin Isra’ilan a matsayin mammunar matakin ingiza tashin hankali. Ya ce wannan hali ya dada bata abinda ya bayyana halin da ake ciki, inda yake shagube da kama sojan Isra’ila da mayakan sa kai na palasdinu suka yi.

XS
SM
MD
LG