Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila tana zafafa kai hari kan kasar Lebanon


Isra’ila ta kara kaimi wajen kai hare haren da ta yi a kan mayakan sa kai na Hezbullah a helkwatar kungiyar dake birnin Beirut a wannan rana ta juma’a da yammaci. Gitan Talbijin na kungiyar Hezbullah ya ce shuganan mayakan sa kai na kungiayr Hassan Nasrallah yana nan lafiya kuma ya yi jawabi wand agidan Talbijin din ya nuna. Ya ce kungiyar Hezbullah a shirye take da niyar abinda ya kira yaki a fili tsakaninta da Isra’ila. Y kuma ce sojojin Hezbullah sun lalata wani jirgin rowan yaki na Isra’ila a gabar Teku a Beirut. Isra’ila ta tabbatar cewa an harbi daya daga cikin jiragen yakinta saida ba’a masa lahani sosai ba. Wani wakilin muryar amirka a birnin Beirut ya ce ‘yan kasar Lebanon sunyi ta harba wuta sama suna cewa Allahu Akbar, domin bukin murnar cewa Nasaralla ya tsira da ransa bayan harin na isra’ila. Firayiministan Isra’ila Ehud Olmert ya yi alkawarin ci gaba da kai hare hare akan mayskan sa kan Hezbullah sai ya ga cewa ya nakasasu tukuna kuma sun saki sojojin sa biyu da suka yi garkuwa dasu. Mahukuntan akasar Lebanon sunce jiragen saman yaki na Isra’ila sun kai hari a filin saukar jiragen sama na birnin a ranar Jumma’a a karo na uku kuma sun jefa bam akan wata abbar hanya da ta hade birni Beirut da birnin Damascus na kasar Syria. Mahukuntan kasar Lebanon sun ce akallan an kashe mutane sittin tun daga lokacin da wannan fata ta kaure a ranar Larawa da ta shige. Sojojin Isara’ila 8 sun mutu a wannan gumurzun.

XS
SM
MD
LG