Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush da Tony Blair suna so a tura sojojin kasa da kasa Lebanon


Shugaba Bush na Amirka ya ce shi da firayi-ministan Birtaniya Tony Blair sun tsaida shawara cewa yakamata a tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa zuwa kasar Lebanon domin su taimaka wajen rarraba kayakin jinkai ga wadanda yakin tsakanin Isra’ila da Hezbullah ya shafa. A wannan juma’ar ce shugabannin biyu suka gana a fadar white House ta shugaban Amirka domin su tattauna a kan batutuwa da dama to amman yankin gabas ta tsakiyane akan gaba a ajandar tattaunawa tasu. Shugabannin biyu Tony Blair da George Bush suna famar shan suka da kakkausar harshe tsakanin kasasuhen duniya bisa kasa sa baki da sukayi na tsagaita bude wuta. To amma Mr Bush ya ce dukkansu biyu sun yi imanin cewa yin amfani da wannan damar daukar mataki mai dorewa akan rikicin gabas ta tsakiya wanda daga karshensa zai bada damar kafa kasa ta Palasdinawa a yankin. Dukkansu biyun sun nanata bukatar da ke akwai ta baiwa gwamnatin kasar Lebanon baya a kokarin samun abinda Mr Bush ya kira cikakken iko a wannan yanki.

Mr Bush ya ce sakatariyar harkokin wajen amirka Condolizza Rice zata sake komawa yankin gabas ta tsarkiya a ranar Asabar domin ta shirya yadda za’a tura sojojin kasa da kasa yankin. Ya ce kwamitin sulhu na MDD zai zauna a makon gobe domin shata jaddawalin yadda za’a kawo karshen zaman gaba tsakanin su.

XS
SM
MD
LG