Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kundun balan Isra'ila sun kama wasu mayakan 'yan Hezbullah biyar


Sojojin kundun balan Isra’ila sun kame mayakan Hezbullah biyar a cikin kasar Lebanon a daidai lokacin da mayakan Hezbullah suke harba Karin rokoki dari da sittin cikin Isra’ila. Isra’ila ta ce sojojinta sun kama mayakan Hezbullah kuma sun kashe goma a wani sumame da suka kai cikin birnin Baalbek kusa da kan iyakar kasar da Syria. Kungiyar Hezbullah ta ce wadanda Isra’ilan ta kama fararen hula ne. Jami’an kasar Lebanon sunce Isra’ila ta kashe fararen hula goma sha biyar a wannan sumamen. Wasu hare haren Isra’ilan ta jiragen sama sun lalata wani karamin sansanin soja a kauyen Sarba sun kashe sojojin kasar Lebanon uku. Sannan dubban sojojin kasa na Isra’ila suna gwabzawa da ‘yan Hezbullah a yankin kudancin Lebanon. Ahalin da ake ciki kuma jami’an Isra’ila sun ce rokokin Hezbullah sun sauka a garin Nahariya dake kusa da kan iyaka. Wasu rokokin kuma sun fada a wani waje mai nisar Kilomita 70 cikin Isra’ila sannan wasu rokokin sun kauce sun sauka a yammacin kogin Jordan. Firayi ministan Isra’ila Ehud Olmert ya ce Isra’ila zata ci gaba da wannan yakin sai lokacin da aka tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa yankin tukuna.

XS
SM
MD
LG