Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

watakila a tsaida shawara akan rikicin Isra'ila da Hezbulallh


Rahoton Majalisar Dindin Duniya ya ce Jami’an Diplomasiyya daga kasashen Amirka da Faransa sun kusan cimma yarjejeniyar warware banbancin ra’ayi tsakaninsu game da kudurin MDD da zai kawo karshen wannan fada tsakanin Isra’ila da Hezbullah.

Babban abinda ke hana ruwa gudu a shawarar tasu shine yadda za’a janye sojojin Isra’ila ko kuma hanyoyi da za’abi wajen aiwatar da hakan. Kasashen Lebanon da Faransa sun bukaci Isra’ila ta fara janye sojojinta dubu 10 da ta tara yankin kudancin kasar sannan Lebanon ta tura nata sojoji wajen. Isra’ila mai samun goyon bayan Amirka ta nace akan sai sojojinta su ci gaba da zama a kasar Lebanon har sai lokacin da sojojin kasa da kasa wadanda ake jin na kasar Faransa ne suka isa yankin.

Jakadan kasar Ghana a kuma shugaban kwamitin sulhu na MDD na wannan wata Nana Effa Apentang ya ce ‘yan kwamitin sulhun basu san matsayin da shawarwarinsu yake ciki ba, kuma sun bukaci kasashen biyu dake da sabanin ra’ayi wadanda kuma suka gabatar da muhawarar akan su fadakar dasu abinda suke ciki. Ya fadawa manema labarai cewa baya son fadawa cikin wasu maganganun zaci fadi, a yanzu haka dukkanmu mun san cewa ana mawuyacin hali.

Shawarwarin da suke yi mai sarkakiyane, dukkansu mun san cewa akwai wata tangarda kuma ina jin cewa suna kokari ne na warwareta. Mai magana da yawun MDD Stephane Durjarric ya ce kakakin MDD Koffi Annan, yana ta tuntubar jami’an Isra’la da Lebanon da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta wayar tarho yana kokarin tura wannan shiri zuwa wani mataki na gaba. Yace Kakakin MDD yana aiki tukuru tsakaninsa da membobin kwamitin sulhu na MDD da kuma manyan shugabanni akan wannan lamari a birnin NY da kuma manyan biranen kasashen a wani kokari na tura wannan kuduri da ya shafi wadannan kasshe biyu.

Ya sake nanata kiranta ya yi akan cewa dolene a dakatar da wannan fada domin a kare lafiya da kuma cire fararen hula daga zullumin fargaba da zaman firgita da suke fuskanta cikin makonni 4 da akayi ana wannan fada a duk bangarorin biyu. Sakataren na MDD yace yayi imanin cewa tana yiwuwa kwamitin sulhu na MDD ya tsaida shawara akan wannan kuduri nan da karshen wannan

XS
SM
MD
LG