Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe 'yan Iraq da dama a wani harin bam na kunar bakin wake


Jami’an Iraq da na Amirka sunce ‘yan gwagwarmaya sun kai hare hare kuma sun kashe ‘yan kasar Iraq 11 da Amirkawa 2. Wani Bam na cikin mota da ya tashi a kasuwa anguwar Sadar na birnin Bagadaza ya kashe akallan mutane 4 a jiya Alhamis sannan fiye da 20 sun ji rauni.

Wani tashin bam din kuma a birnin ya jiwa mutane da dama rauni. A yankin arewacin kasar kuma, wasu mahara sun kai hari a ciki da wajen garin Baquba, sun kashe a kallan mutane 6 kuma an harbi wani sojan Iraq dake gadin waje mai man Fetur, ya mutu.

XS
SM
MD
LG