Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Rasha sunce wani jirgin pasinja dauke da mutane 170 ya fadi a gabashin kasar Ukraine.


Hukumomin Rasha sunce wani jirgin pasinja dauke da mutane 170 ya fadi a gabashin kasar Ukraine. Hukumar aiyukkan gaggawa ta Rasha tace wannan jirgin, kirar Tupolev (TU-154) ya fito ne daga wurin shakatawar Anapa ne kan hanyarsa ta zuwa birnin Petersrburg, lokacinda yayo sulu zuwa kasa.

Kafofin watsa labaran Rashar sunce kananan jirage masu saukar ungulu dake shawagi a sararin dake daidai da inda abin ya faru, kamar km 45 arewa da garin Donbetsk na kasar Ukraine din, sunce sun hango gawar jirgin a kasa, yana ta ci da wuta. Kuma rahottanin farko da suka fara shigo mana sunce izuwa yanzun an riga an tsamo gawwawakin mutane kamar 30. Kafar watsa labarai ta Interfax ta ruwaito wani jami’in sufurin jiragen saman Rasha mai suna Alexander Neradko yana cewa jirgin ya fadi ne bayanda ya fsukanci wani irin tangal-tangal yayinda yake can sama.

XS
SM
MD
LG