Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta maido wa kasdashen Turai amsa ga tayin da suka yi mata


Iran ta maido wa kasdashen Turai amsa ga tayin da suka yi mata na bata wasu abubuwan don ta jingine kudurinta na neman fasahar nukiliya, don ta nunawa duniya bata da wani abin jin tsoro. Dazu-dazu ne babban jigon aiyukkan nukiliya na Iran din, Ali Larjani ya mika takardar dake kunshe da amsar tasu ga wani manzannin dake wakiltar kasashen nan biyar masu waskilicin dindin akan kwamitin tsaron MDD da Jamus.

Sai dai a halin yanzu ba’a san abinda bayanin ya kunsa ba, to amma an san cewa tun jiya Litinin shugaban addini na Iran din, Ayatollah Ali Khamenei ya riga ya fito fili ya bayyana niyyar Iran na ci gaba da neman wannan fasahar ta nukiliya, koda yake kuma ya sake fayyace cewa ba fa makaman nukiliya suke nema ba.

XS
SM
MD
LG