Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Ahmadin Nejad na Parisa ya bijirewa wa'adin MDD


Shugaban kasar Parisa wato Iran, Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana bijirewa, a daidai lokacin da wani wa’adin da MDD ta bawa Iran cewa ta dakatar da ayyukanta na nukiliya masu tada hankali, ya ke shirin cika. A jiya talata a birnin Tehran Mr. Ahmadinejad ya fada cewa babu wanda zai hana Iran mallakar shirin nukiliyar yin ayyukan zaman lafiya.

Haka kuma ya ce babu alamun cewa kwamitin sulhun MDD zai dauki wani mataki game da kasar Iran. Gwamnatin kasar Iran na fuskantar wani wa’adin da kamitin ya ba ta, wanda zai cika a gobe alhamis cewa ta daina ayyukan ta na tace ma’adinin uranium, in kuwa ba haka ta ci karo da yiwuwar daukan matakan ladabtar da ita. A nan birnin Washington DC, wani kakakin ma’aikatar harakokin wajen Amurka mai suna Tom Casey ya fada cewa ya na kyautata cikakken zato za a dauki matakan ladabtar da Iran idan ta kasa yin aiki da wa’adin da aka ba ta. Amma ya ki bada wani lokaci na takaimaimai da matakan za su fara aiki.

Kasashen yammacin duniya na zargin Iran da kokarin kera makaman nukiliya. Iran ta ce shirin na nukiliya ba na wani abu ba ne illa kawai samar da wutar lantarki.

XS
SM
MD
LG