Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Levy Mwanawasa Na Zambiya Yayi Rokon A Kwantar Da Hankula


Shugaba Levy Mwanawasa na Zambiya yayi rokon da a kwantar da hankula a cikin jawabin da yayi ga al’ummar kasar kafin a fito da cikakken sakamakon zabe.

Hukumar zabe ta Zambiya ta fito da wani bangaren sakamakon zaben jiya lahadi, wanda ya nuna Mr. Mwanawasa a gaba da kashi 42 cikin 100 na kuri’un da aka jefa. Shugaban jam’iyyar United Democratic Alliance, Hichilema Haikande, yana matsayi na biyu da kashi 28 daga cikin 100, yayin da jam’iyyar Patriotic Front ta mutumin da ake dauka a zaman babban mai kalubalantar shugaban, Michael Sata, take matsayi na uku da kashi 27 daga cikin 100.

Magoya bayan Mr. Sata sun fusata da jin cewa yana matsayi na uku, suka kona ababen hawa tare da jifar ’yan sanda da duwatsu a unguwanni da dama na talakawa. Har ila yau ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a kan ’yan zanga zanga a kofar babbar cibiyar kidaya kuri’u a Lusaka. An kama ’yan zanga zanga da dama.

Mr. sata ya ce an tabka magudi a zaben na ranar alhamis.

XS
SM
MD
LG