Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamandan Sojojin Rasha A Yankin Tsaunukan Caucasus Ya Ce Dakarunsu Dake Georgia Zasu Yi Amfani Da Karfi Mafi Tsanani...


Kwamandan sojojin Rasha a yankin tsaunukan Caucasus, Janar Andrei Popov, ya ce sojojin Rasha zasu yi amfani da karfi mafi tsanani domin kare sansanonin sojansu dake kasar Georgia. Zaman doya da manja ta kara tsanani tun lokacin da Georgia ta kama wasu hafsoshin sojan Rasha su hudu tana zarginsu da laifin leken asiri.

Wakilin Muryar Amurka a Moscow, Bill Gasperini, ya ambaci shugaba Vladimir Putin na Rasha yana bayyana kama sojojin kasarsa da Georgia ta yi a zaman ta’addanci.

An jima ana zaman tankiya a dangantakar Rasha da makwabciyarta ta kudu, Georgia. Amma a cikin ’yan kwanaki kalilan da suka shige, dangantakarsu ta kara yin tsami a sanadin kama wadannan sojoji an Rasha da Georgia ta yi tana zarginsu da laifin leken asiri.

A ranar asabar, Rasha ta bayar da sanarwar cewa zata dakatar da janye sojojinta da take yi sannu kan hankali daga sansanonin sojan zamanin Tarayyar Soviet a Georgia, tana mai fadin cewa watakila za a bukace su a saboda yadda lamuran tsaro suke sukurkucewa. Har ila yau Rasha ta bayar da umurnin kwashe ma’aikatan ofishin jakadancinta dake Tbilisi, babban birnin Georgia, tana mai fadin cewa su na cikin hatsari a jamhuriyar dake tsaunukan Caucasus.

’Yan sandan Georgia sun kewaye wani sansanin sojan Rasha dake Tbilisi, yayin da gidan telebijin na kasar ya nuna wani hoton bidiyo inda ’yan Rasha da aka kama suke ganawa da wasu ’yan Georgia da aka ce masu yi musu leken asirin ne. A ranar jumma’a, wata kotun Georgia ta bayar da umurnin da a tsare sojojin hudu na Rasha na tsawon watanni biyu har sai an ji sakamakon wani bincike, koda yake ministan tsaron Georgia ya ce ana iya kyale mutanen su hudu su koma kasarsu Rasha.

Manyan jami’ai daga kasashen waje, ciki har da Amurka, sun buga waya ma shugaba Mikhail Saakashvili na Georgia mai ra’ayin kasashen yammaci, suna kiransa da a kai zuciya nesa.

Dangantaka a tsakanin Rasha da Georgia ta yi ta sukurkucewa tun lokacin da Saakashvili ya hau kan karagar mulki a wani juyin juya halin da ake kira "Rose Revolution" shekaru uku da suka shige. Shugaban na Georgia, wanda yayi karatu a nan Amurka, ya sha yin magana kan kwadayin ganin Georgia ta shiga kungiyar kawancen tsaron NATO, matakin da ya harzuka kasar Rasha.

Har ila yau kasashen biyu suna sabani a kan makomar wasu yankuna biyu masu neman ballewa daga kasar Georgia, wadanda suka jima suna samun tallafin kudi da na siyasa daga Rasha.

XS
SM
MD
LG