Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Ce Ta Yi Gwajin Makamin Nukiliya


Koriya ta Arewa ta ce ta yi gwajin makamin nukiliya a karkashin kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa ya bayyana cewar an samu nasarar wannan gwajin makamin nukiliya da aka gudanar yau litinin da safe, ya kuma ce babu wani tururi na nukiliya dake yoyo a yankin.

jami'an tsaro na Koriya ta Kudu, makwabciyar Koriya ta Arewa, sun ce an gudanar da wannan gwajin ne a Hwaderi kusa da birnin Kilju yau litinin da safe. Koriya ta Kudu ta ce ta auna motsin kasa mai karfin awu 3 da digo 6 a Koriya ta Arewa a daidai lokacin da aka ce an gudanar da wannan gwaji (da karfe 2 da minti 36 na dare agogon Nijeriya).

Shugaba Roh Moo-hyun na Koriya ta Kudu ya kira taron tsaro na gaggawa domin tattauna wannan batu.

Har yanzu jami'an Amurka ba su tabbatar da ko sun ga alamun gwajin ba.

A makon jiya Koriya ta Arewa ta yi gargadin cewa zata yi gwajin makamin nukiliya domin karfafa tsaronta daga abinda take bayyanawa a zaman kiyayyar da Amurka take nuna mata.

Wannan gwajin da Koriya ta Arewa ta gudanar ya haddasa kai gwauro da mari a fagen diflomasiyya a fadin duniya.

XS
SM
MD
LG