Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban jammi’i mai shiga tsakani na Amurika a game da shirin nukliyar Korea ta arewa yana Japan domin tataunawa


Babban jammi’i mai shiga tsakani na Amurika a game da shirin nukliyar Korea ta arewa yana Japan domin tataunawa a daidai lokacinda kassashen yankunan suka soma wani sabon bincike da yiwuwar kakaba ma gwamnatin Pyongyang takunkumi. Mataimakin Sakatariyar harakokin wajen, Amurika Christopher Hill ya gana da takwaran aikin sa na Japan Kenichiro Sasae, kafin wani sabon yunkuri na kokarin da kassashe shidda za su yi domin tatauna batun wargaza shirin makaman nukliyar gwamnatin Pyongyang.

A yau Litinin ma, ministan harakokin wajen Australia Alexander Downer ya ce kasar sa ta hana jiragen ruwan Korea ta arewa bi ta mashigar gabar Australia a sakamakon gwajin makamaman nukliyar da ta yi ikirarin ta yi makon da ya gabata. Wani lokaci a cikin makon nan, sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleeza Rice za takai ziyara a Japan da Koriya Ta arewa domin tataunawa akan lallashin gwamnatin Pyongyang ta koma kan teburin sasantawa.

Kwamitin sulhun MDD ya amince da kakaba ma Korea ta kudu takunkumi ranar Asabar tare da kira ga gwamnatin Pyongyang akan ta kawo karshen ayyukan nukliyar ta. To amma bayan kada kuri’ar, kasar China ta ce tana adawa da bukata daga mambobin MDD na binciken motoci masu shiga ko fita daga Korea ta arewa

XS
SM
MD
LG