Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Amirka sun tabbatar cewa Koriya ta Arewa ta gwada makamin Nukiliya


Jami’an Hukumar Leken asirin Amirka sun tabbatar cewa lallai kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin Nukiliya a karkashin kasa a makon jiya. Wata sanarwa daga darektan hukumar Leken asiri na cikin kasa ta ce an gano wani tururin makaman nukiyar a samfurin iska da aka dauko wadanda ya tabbatar da an gwada makamin nukiliya madaidaici mai karfin kiloton guda. Wannan sanarwa tayi kicibis da daidai lokacin da sakatariyar harkokin wajen Amirka Kondoleezza Rice take haramar tashi a yau Talata zawa ziyarar kasashen dake makobtaka da kasar Koriya ta Arewa domin tattaunawa akan yadda za’a aiwatar da sharrudan takunkunim da MDD zata kafawa kasar Koriya da kuma kokarin janyo ra’ayin kasar ta koma kan teburin shawarwari kan batun nukiliyarta.

SHUGABA BUSH YA TAYA AMIRKAWA MUSULMI BUDE BAKI A FADARSA

Shugaba Bush na Amirka ya marabci shugabannin addinin Islama a fadarsa ta White House jiya Litinin da yamma domin buda baki . Wakiliyar MA Paul Wlfson ta aiko mana rahoton cewa daga cikin bakin shugaban harda Amirkawa musulmi wadanda suke aiki a matsayin ‘yan kwana-kwana da ‘yansanda da kuma wadanda suka aikin soja.XS
SM
MD
LG