Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amirka zata baiwa 'yan gudun hijira dubu 10 mafaka


Amirka ta yi alkawari zata baiwa 'yan kasar Burundi dubu 10 matsuguni a matsayin 'yan kasa a Amirka. wasu da gacikin ‘yan kasar Burundi da aka amincewa su zauna a nan amirka sun fice daga kasar a shekara ta 1972, kuma sun zauna a wasu kasashe uku cikin shekaru da suka wuce. Daga cikin kasashen harda kasar Rwanda da Janhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma kasar Tanzania. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amirka Tom Casey yace amirka ta yanke shawara ta karbi ‘yan gudun hijiran kasar Burundin ne bayan wata kira da kwamishinan ‘yan gudun hijira na MDD tare da hadin guiwar gwamnatin kasar Tanzaniya suka mata. Ya ce ko shakka babu Wannan wani tsohon batune da ya jima ana yinsa. Amirka ta amsa kiran da kwamishinan ‘yan gudun hijira yayi mata bayanda ta nazarci nazarci halin da wadannan ‘yan gudun hijira suke ciki. Kuma duk da ganin akwai tsohon tarihi akan wadannan mutane, da suka shafi batun basu mazauni da sake kauratar da su da wasu matsalolin dubawa, wadanda suka jinkirta wannan lamari, amirka a shekarar bara ta sami bukatar basu matsuguni, don haka ne ta dauki mataki ayanzu. Kowa da cikin wadannan‘yan gudun hijira da aka amince za’a ba shi masauki anan Amirka, sai jami’an ma’aikatar tsaron cikin gida sun yi masa tambayoyi tukuna domin tabbatar da cancantarsa. Da zaran an gama musu tababaya za’a basu damar neman kasancewa ‘yan kasa a Amirka. Steve Corlis jami’in hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD a birnin Daressalam na kasar Tanzania, yace Amirka tana da shirin mai kyau na sake tsugunar da ‘yan gudun hijiran.

XS
SM
MD
LG