Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Rattaba Hannu Kan yarjejeniyar Zaman Lafiya Da 'Yan Tawayen Gabashin Kasar


Gwamnatin Sudan ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen gabashin kasar da nufin kawo karshen tawayen shekaru goma da ake yi a wannan yanki.

Wani kakakin gwamnati ya ce a yau laraba ne majalisar zartaswar kasar ta amince da wannan yarjejeniya a wani zama na musamman da shugaba Hassan Omar al-Bashir ya jagoranta.

Shugaban ya ce a cikin kwanaki biyu za a dage dokar-ta-bacin da ake aiki da ita a yankin gabashin Sudan.

Gwamnati da shugabannin 'yan tawaye sun sanya hannu a kan yarjejeniyar ranar asabar tare da taimakon masu shiga tsakani na Eritrea.

A karkashin yarjejeniyar, gwamnati zata shigar da mayakan 'yan tawayen gabashin Sudan a cikin rundunar sojojinta, zata kuma nada 'ya'yan kungiyar da dama bisa mukamai na gwamnati.

Haka kuma a cikin shekaru biyar masu zuwa, gwamnati zata samar da kudi dala miliyan dari shida wanda za a yi amfani da shi wajen raya yankin na gabashin Sudan.

A cikin shekarun 1990 ne 'yan tawayen gabashin Sudan suka dauki makamai suka fara yakar gwamnati, bisa zargin cewa ta yi watsi da yankin nasu. Yankin yana da albarkatun kasa sosai, amma kuma yana fama da talauci. Yankin ya kunshi kabilar Beja wadda ba jinsin larabawa ba ce, da kuma kabilar Rashaidya wadda ta larabawa ce.

XS
SM
MD
LG