Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan, ya ce ya kamata a bai wa  Ivory Coast damar karshe ta gudanar da zabe


Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce ya kamata a bai wa shugabannin kasar Ivory Coast damar karshe ta gudanar da zabe, amma kuma idan sun kasa to tilas ne kasashen duniya su tsoma hannu.

A cikin wani rahoton da aka rarrabawa wakilan Kwamitin Sulhu jiya laraba, Mr. Annan ya soki shugabannin siyasa na Ivory Coast da kakkausar harshe, yana mai dora musu laifin jinkirta zabe a karo na biyu cikin shekara guda. Babban jami’in sanya idanu kan harkokin zabe na MDD a kasar Ivory Coast, ya ce za a jinkirta zabe har zuwa watan Oktobar 2007.

Mr. Annan ya ce idan har ba a gudanar da zabe a cikin shekara mai zuwa ba, to ya kamata MDD da shugabannin Afirka su yi tunanin kafa gwamnatin rikon kwarya wadda zata kunshi sanannun ’yan kasar wadanda ba su goyon bayan wata jam’iyya ko akidar siyasa. Ana daukar zaben da aka jima ana sa ran gudanarwa a zaman mai muhimmanci wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasar dake yankin Afirka ta yamma.

XS
SM
MD
LG