Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo ya kafa Dokar ta baci a Jahar Ekiti


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya ayyana kafa dokar-ta-baci a Jihar Eikiti dake yankin kudu maso yammacin kasar, a bayan abinda ya kira tsige gwamnan Jihar ta hanyar haramun da aka yi.

Wakilin Muryar Amurka a Abuja, ya ambaci shugaban yana fadi cikin wani jawabin da yayi ta gidan telebijin ga al'ummar Nijeriya cewa wannan rikici na Ekiti yana yin barazana ga zaman lafiya da harkar tsaro na kasar baki daya. Gwamnan jihar da mataimakiyarsa, wadanda wai yan majalisar jihar suka tsige su ranar litinin, tare da shi wannan mai cewa shike rike da
mukamin Gwamna ganin sun tsige Peter Ayo Fayoshe,da kuma ita majalisar kanta yanzu duka an jingine su ba tare da bata lokaci ba.

Shugaba Obasanjo ya nada wani Janar na soja mai ritaya, Tunji Olurin, ya
jagoranci jihar na tsawon wata 6. Kafa dokar ta bacin dama an zaci hakan, kuma daukar matakin kusan yana tabbatarda rade radin cewa dama niyyar gwamnatin tarayya ce ta iza wutar wannan fitinar domin ta sami sukunin kafa dokar ta-bacin gabannin zabemai gabatowa a badi.

Maxi Okwu mutum ne dake lura da lamuran siyasa a Abuja. Ya ce, "...An
tafiyarda wannan lamari kamar yadda aka tsara. Wannan daga sama aka
shiryashi. Gwamnatin tarayya ce ta tsara wannan lamari,domin idan kaga
wadda ke cewa shine mukaddashin Gwamna kuma yana samun tsaro da kariya
sai ka tambayi kanka da kanka. Babu yadda za'ayi kwamishinan yan sanda ya yanke shawara irin wannan ba tareda ya sami umurni daga hukumomi daga tarayya ba. Dama domin a haifarda wannan rikicine don a sami sukunin kafa dokar ta baci. Babu tabarbarewar doka da oda."

A maida martini kan rade rade gameda manufar gwamnati, shugaba Obasanjo ya dage cewa bashi da nufin ci gaba bayan wa'adin mulkinsa ya kare. A farkon wannan shekara ce Majalisar dokoki ta kasa tayi fatali da
yunkurin yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasa da aka nemi yi domin
baiwa Obsanjo damar ya tsaya zabe a karo na 3.

Jami'an soja da yan sanda suna sintiri kan titunan Ado Ekiti fadar
Jihar,domin kwantarda duk wata fitina. Gwamnonin jihohin jihar Anambara
dake kudu maso gabas da jihar Plateau dake tsakiya suma suna fiskantar barazanar a tsigesu,wadda masu lura da lamura suke ganin zai kara harzuga al'amura.
XS
SM
MD
LG