Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Koka Da Kakkausar harshe Kan kalamun Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Kasar


Sudan ta koka da kakkausar harshe ga wakilin majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar, Jan Pronk, dangane da furucinsa na cewar guiwar sojojin gwamnatin Sudan ta mace.

A cikin wata sanarwar da ya bayar yau jumma'a, kamfanin dillancin labaran Sudan ya ce wannan furuci na Mr. Pronk wuce makadi da rawa ne a matsayinsa na wakilin MDD. Sanarwar ba ta ce uffan ba game da rahotannin da aka samu tun farko cewa an umurci Mr. Pronk da ya tattara nasa ya nasa ya bar kasar ta Sudan.

A makon jiya Mr. Pronk ya rubuta a cikin adndalinsa na kansa a duniyar gizo cewa 'yan tawaye sun bada sojojin gwamnati kashi a wasu fadace-fadace biyu manya da aka yi a yankin Darfur. Har ila yau ya ce rundunar sojojin Sudan ta kori wasu manyan janar-janar, yayin da wasu sojojin ma suka ki yarda su shiga cikin fada a Darfur.

A cikin hirar da yayi da VOA, wani kakakin rundunar sojan Sudan ya musanta wannan ikirari an Mr. Pronk. Har ila yau ya zargi jami'in an MDD da laifin yin katsalanda a harkokin sojan Sudan.

A cikin watan Agusta gwamnatin Sudan ta kaddamar da farmakin soja a kan 'yan tawayen da ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar kulla zaman lafiya da gwamnati ba a yankin Darfur.

XS
SM
MD
LG