Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Chadi Ta Ce Sojojinta Sun Fatattaki Harin Da 'Yan Tawaye Suka Kai Kan Wasu Garuruwa Biyu


Gwamnatin Chadi ta ce sojojinta sun fatattaki hare-haren da 'yan tawaye suka kai kan wasu garuruwa biyu a yankin gabashin kasar.

Ma'aikatan agaji a gabashin Chadi sun ce 'yan tawaye sun shiga garin Goz Beida ranar lahadi, suka yi ta harbi a sama.

Gwamnatin Chadi ta ce sojojinta sun kwato yankin, daga baya kuma suka kwato wani gari a kusa da nan. Ba a bayar da rahoton hasarar rai ba.

Wasu kungiyoyin 'yan tawaye uku masu adawa da shugaba Idris Deby na Chadi sun bayar da sanarwar cewa zasu kafa sabon kawance. Amma kuma wani mai fashin bakin al'amuran yankin ya ce a can baya irin wannan hadin kai bai dore ba a saboda rarrabuwar kawuna ta kabilanci.

XS
SM
MD
LG