Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yan sandan Iraqi 24 da mayakan sa kan Iraqi goma sha takwas aka kashe


Rundunar sojin Amurka a Iraqi ta bada labarin cewar ’yan sandan Iraqi ashirin da hudu da mayaƙan sa kan Iraqi goma sha takwas ne aka kashe a wani gumurzun yaƙin da aka yi a zagayen birnin Baquba.

Kazalika, an kashe farar hula bayan da mayaƙan sa kai suka yiwa ’yan sandan Iraqin kwanton ɓauna jiya Alhamis. A can Arewacin birnin Mosul kuma, hukumomin Iraqi sun sanya dokar zirga-zirgar motoci bayan da mayaƙan sa kai suka rarraba takardun dake barazanar tada zaune tsaye a yankin dake tattare da al’ummar Larabawa da Kurdawa.

Haƙiƙa wannan wata na Oktoba inji mai magana da yawun rundunar sojin Amurka, wata ne da rundunar sojin Amurka ta haɗu da babban rashin sojinta indaaka kashe mata soja 96.

XS
SM
MD
LG