Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Dakatar Da Shirin Korar Dubban Larabawa 'Yan Chadi


Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da shirin korar dubban larabawa makiyaya 'yan kasar Chadi.

A yau Jumma'a jami'ai suka bayyana wannan shawara, suka kuma ce za a tura tawagar gwamnati domin ta gana da shugabannin larabawan a yankin kudu maso gabashin kasar.

A ranar talata Nijar ta ce zata kori Larabawan jinsin Mahamid har su dubu dari daya daga kasarta. Amma daga baya jami'ai suka ce wannan umurnin kora ya shafi wadanda ba su da takardun zama akasar ne kawai, wadanda kuma yawansu ya kai dubu uku zuwa hudu.

Gwamnatin Chadi ta soki Nijar a saboda ba ta sanar da ita da wuri cewar zata kori wadannan 'yan gudun hijira ba. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka ce wannan kora zata keta hakkin 'yan gudun hijira.

Gwamnatin Nijar tana zargin larabawa makiyayan da laifin rike makamai da kuma gurbata muhalli a yankin gabashin kasar. Wadannan larabawa makiyaya sun fara gudu daga kasar Chadi a shekarun 1970 domin tserewa kwamfar ruwa da kuma rashin kwanciyar hankalin siyasa a kasar tasu.

XS
SM
MD
LG