Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakkwatawa Da Ma Sauran 'Yan Nijeriya Su Na Jimamin Rasuwar Sultan Muhammadu Maccido


Sakkwatawa da sauran al'ummar Nijeriya su na jimamin rasuwar Sultan Muhammadu Maccido da sauran manyan 'yan siyasa da jami'ai na Jihar Sakkwato wadanda suka rasu a lokacin da jirgin saman kamfanin ADC ya fadi a Abuja.

Wakilanmu a Abuja da Sakkwato sun aiko mana da rahotanni a kan yadda wannan jirgi ya fadi, da irin mutanen dake cikinsa, da kuma irin girgizar da al'ummar Nijeriya suka yi da wannan hatsarin.

A cikin wadannan rahotanni da za a iya ji a sama, Umar Faruq Musa daga Abuja, da Aminu Bello Sahabi daga Sakkwato, da babban limamin masallacin Abuja, Musa Muhammad Inuwa, da Hussaini Zakariya daga Abuja duk sun yi magana game da hatsarin.

XS
SM
MD
LG