Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira da adauki kwararan matakai na garanbawul..


Mataimakin shugaban Nigeria Alhj. Atiku Abubakar ya ce matakin farko na da za’a dauka wajen gyaran wannan ma’aikata mai tarin matsala, shine cigaba da bincika lafiyar jiragen sama masu sintiri cikin kasar ko da ya kama a kowace rana za’ayi. Yace hakan za ta taimawa wajen tabbatar da lafiyar jiragen sake daukar fasinjojinmu a kullun rana. Su kuma kamfanonin sintirin jiragen sama a kafa musu dokoki masu tsanani.

Jami’an Nigeria sunce wakilan kamfanonin kera jiragen sama na Boeing da kuma na kamfanin Pratt & Whiteney dake kera injin jiragen sama za su je Nigeria ranar Talata domin taimakawa wajen binciken muabbabin wannan hatsari na ranar Lahadi da ya ci rayukan ‘yan Najerriya sama da 98. Haka kuma wakilan hukumar kula da lafiyar jiragen saman fasinja ta kasa da kasa za su je Nigeria a makon gobe domin duba lafiyar jiragen saman fasinja a kasar.

Wannan hatsarin jirjin sama na baya bayan nan shi ya kara adadin wadanda suka rasa rayukansu a faduwar jiragen sama a Najeriya cikin shekaru uku da suka wuce zuwa fiye da mutum dari uku. An dorawa kuskuren dan adam da munin yanayi laifin faduwar jirgin saman kamfanin jiragen sama na Sosoliso samfurin DC-9 na watan Disamban bara inda mutane 107 suka rasa rayukansu laifi.

Jami’an hukumar sintirin jiragen sama ta Najeriya sun dorawa matukin jirjin saman kamfanin ADC da ya fadi ranar Lahadi laifin kin aiki da umurni akan kadda ya tashi saboda rashin kyaun yanayi. Duk da haka akasarin ‘yan Nigeria sun sance ma’aikatar sitirin jiragen sama ta Nigeria tanada tsananin ganganci da sakaci kuma tanada hatsari don haka tana bukatar muhimmin garanbawul.

XS
SM
MD
LG