Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Dokokin Somaliya Yace Zai Yi Kokarin Sasanta Gwamnati Da Masu Kishin Islamar Kasar


Kakakin majalisar dokokin Somaliya ya ce zai yi kokarin kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin gwamnati da kungiyar masu kishin Islama mai karfi ta kasar domin kaucewa yaki.

Sharif Hassan Sheikh Aden ya fadawa manema labarai yau Jumma’a a Nairobin Kenya cewa zai gana da shugabannin masu kishin Islama ranar lahadi a Mogadishu wanda ke hannunsu.

Aden ya ce babu daya daga cikin shugaban Somaliya ko Firayim Ministan kasar da ya ba shi iznin kai wannan ziyara. Ba a ji ta bakin gwamnati game da wannan yunkurin kakakin majalisar ba.

A ranar laraba tattaunawa ta wargaje a tsakanin gwamnatin rikon kwarya da ’yan Islama a kasar Sudan.

Shaidu sun ce sassan biyu suna jan damarar gwabzawa a kewayen garin Baidoa inda gwamnatin riko take da hedkwatarta. Wannan gari dake kudancin Somaliya shine kadai yake hannun gwamnatin rikon wadda ba ta da karfi.

Mazauna yankin suka ce dukkan sassan biyu sun girka karin sojoji a wannan yanki, sun kuma yi gwaje-gwajen harba bindigoginsu na igwa cikin ’yan kwanakin nan, abinda ya sa wasu fararen hula suka arce.

XS
SM
MD
LG