Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Kimanin Arba'in Suna Birnin Beijing Da Kansu...


Shugabannin Afirka sun hallara a birnin Beijing domin wani taron koli da manyan shugabannin kasar Sin, wanda ake sa ran zai mayar da hankali a kan karfafa huldar tattalin arziki da ta siyasa.

Gobe asabar za a fara gudanar da wannan taron koli na Afirka da Sin, koda yake tun daga yau jumma’a aka fara taron manyan jami’an sassan biyu.

Ana sa ran cewa a cikin kwanaki biyu da suke tafe, kasar Sin zata bayar da sanarwar wani shirin bayar da agaji tare da yin cinikayya da Afirka. Cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashe 53 na Afirka ta ninku har sau goma a cikin shekaru goman da suka shige, kuma a cikin wannan shekara ana sa ran zata kai ta dala miliyan dubu hamsin.

Wannan taron koli yana daya daga cikin tarurrukan diflomasiyya mafiya girma da kasar Sin ta taba shiryawa a tarihinta. Shugabanni kimanin arba’in daga Afirka zasu halarci taron da kansu.

A cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta samar da kudin gudanar da wasu ayyuka da dama a nahiyar Afirka, kama daga harkar man fetur a Nijeriya da Angola da Sudan, da ta aikin jan karfe a Zambiya da kuma na tonon tama a Afirka ta Kudu.

XS
SM
MD
LG