Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joseph Kabila Ya Lashe Zaben Kwango-Ta-Kinshasa


Hukumar zabe ta kasar Kwango ta Kinshasa ta ayyana shugaba Joseph Kabila a zaman wanda ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasar da aka yi.

A yau laraba hukumar zabe mai zaman kanta ta ce Mr. Kabila ya samu kashi hamsin da takwas daga cikin dari na kuri’un da aka kada, yayin da mataimakin shugaba Jean-Pierre Bemba ya samu kashi arba'in da biyu daga cikin dari.

Cibiyar Carter ta tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, wadda ta sanya idanu kan yadda aka gudanar da zaben, ta ce wannan adadin da aka wallafa yayi daidai da irin adadin da aka tattara a rumfunan zabe. Amma kuma kungiyar ta ce tilas a sake nazarin kundin masu jefa kuri’a da kuma batun sunayen masu jefa kuri’a da aka cire daga kundin kafin ta yanke hukumci a kan sahihancin wannan sakamako.

Kawancen jam’iyyun dake goyon bayan Mr. Bemba ta ce ita ma ta gudanar da nata kidayar, inda ta gano cewar Mr. Bemba ne ya lashe zaben na ranar 29 ga watan Oktoba da kusan kashi hamsin da uku daga cikin dari na kuri’un da aka jefa. Gamayyar jam’iyyun ta zargi hukumar zabe da laifin yin ha’inci a lokacin kidayar kuri’un.

Har ila yau magoya bayan Mr. Bemba sun yi gargadin cewa za su yi watsi da yarjejeniyar da suka kulla da bangaren Mr. Kabila cewar zasu yi na’am da sakamakon zaben cikin lumana. A ranar asabar an yi arangama a tsakanin magoya bayan Bemba da na Kabila a titunan Kinshasa har aka kashe mutane akalla hudu.

XS
SM
MD
LG