Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Iraqi Sun Ce An Sako Biyu Daga Cikin 'Yan Yammaci Biyar Da Aka Sace Ranar Alhamis


Jami'an Iraqi sun ce an kwato biyu daga cikin ’yan kwangilar tsaro su biyar 'yan kasashen yammaci da aka sace jiya alhamis, yayin da aka tsinci gawar guda daga cikinsu.

Jami'an suka ce an kwato mutanen biyu yau Jumma'a a sumamen da ’yan sanda suka kai a wani yanki mai suna al-Dawajin a kudancin Iraqi.

Jiya alhamis wasu 'yan bindiga suka sace 'yan kwangilar su biyar, hudu Amurkawa mutum guda dan kasar Austriya, daga cikin wata kwambar motoci a kusa da birnin Basra a kudancin Iraqi. Ba a fahimci ko su wanene daga cikin 'yan kwangilar biyar aka kwato ba, ko kuma wanda ya rasa ransa. .

Akwai wasu mutanen su tara dake tafiya cikin kwambar motoci guda da 'yan kwangilar wadanda ba a sace su ba, ciki har da 'yan kasashen Indiya, Pakistan da Philippines.

A wani lamarin dabam kuma, rundunar sojoji ta ce an kashe wani sojan Amurka daya jiya alhamis lokacin arangama a lardin Diyala a arewacin Iraqi.

A halin da ake ciki, wani babban malami dan mazhabin Sunni, ya ce takardar iznin kama shin da gwamnatin Iraqi ta bayar ta haramun ce. Harith al-Dari, ya fada yau Jumma'a daga birnin Amman a kasar Jordan cewar zai koma Iraqi a lokacin da ya ce ya dace. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraqi ta ce ana neman al-Dari a saboda zargin yana goyon bayan ta'addanci.

XS
SM
MD
LG